1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da neman kawar da gwamnatin Masar

February 8, 2011

Har yanzu babu sararawa tsakanin gwamnati da masu bore neman Mubarak ya sauka da ga mulki,

https://p.dw.com/p/10DnK
Masu boren neman a kawar da Husni Mubarak a dandalin TahrirHoto: dapd

An shiga zagaye na biyu a tattaunawa tsakanin 'yan adawa da gwamnatin ƙasar Masar, wadda ke fiskantar turjiya daga miliyoyin masu bore. Ko da a wannan Talatar ma dai masu boren sun yi kira da a ƙara jajurcewa a dandalin Tahrir dake birnin Alƙahira, har sai an kawar da gwamnatin Husni Mubarak. Masu adawan sun nuna takaici bisa yadda aka gudanar da tattaunawar farko a ƙarshen mako, tare da mataimakin shugaban ƙasa Umar Sulaiman wanda aka naɗa bayan fara boren, inda suka ce tattaunawar ba ta tsinanan komai ba. Ɓangaren adawa mafi ƙarfi na Yan'uwa Musulmai wato Muslim Brotherhood, suka ce babu abinda aka yi, kan buƙatunsu waɗanda suka haɗa da yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulki ƙasar da baiwa 'yan jaridu 'yancin gudanar da aikinsu da kuma ɗage dokar ta ɓaci.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammad Nasiru Awal