1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farautar maharan Brussels

Zainab Mohammed Abubakar / LMJMarch 23, 2016

Jami'an tsaro a Beljiyam sun dukafa wajen laluben wani mutum da hotonsa ya fito a filin sauka da tashin jiragen sama na Brussels tare da wasu mutane biyu.

https://p.dw.com/p/1IITE
Birnin Brussels na kasar Beljiyam ya fuskanci harin ta'addanci
Birnin Brussels na kasar Beljiyam ya fuskanci harin ta'addanciHoto: Getty Images/C. Furlong

Ana dai zargin mutanen da hannu a harin da aka kai a birnin Paris na kasar Faransa a shekarar da ta gabata ta 2015. Nahiyar Turai dai na cikin wani yanayi na alhini da tsaurara matakan tsaro biyo bayan harin aka fuskanta a birnin Brussels din wanda kawo yanzu aka tabbatar ya hallaka mutane 34 tare da raunata wasu sama da 200. Kungiyar IS wadda ta dauki alhakin harin birnin Paris, a wannan karon ma ta ce harin birnin na Brussels aikinta ne. Hakan dai na nuni da cewar kungiyar na neman yada fafutukarta a nahiyar Turai, baya ga yankin Gabas ta Tsakiya da yanzu take neman mamayewa.

Zaman makoki na kwanaki uku

An dai kaddmar da zaman makoki na kwanaki uku a kasar ta Beljiyam. A ma'aikatun gwamnati da makarantu da har ma cikin gidaje, jama'a sun yi shuru na minti guda a wani mataki na karrama mutanen da rayukansu suka salwanta a hare-haren. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel Jamus Merkel wadda ta jajantawa hukumomin kasar ta Beljiyam ta ce:

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merke
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: picture-alliance/dpa/K. Nietfeld

"Wadannan suka yi wannan aika aikan makiyan manufofin nahiyar Turai ne da abin da ya hada kawunanmu a matsayin mambobin kungiyar Tarayyar Turai. Hadin kanmu ne kawai zai karfafe mu, kazalika walwalarmu za ta samu nasara a kan ta'addanci."

Farautar 'yan ta'adda

Jami'an 'yan sanda sun gudanar da samame cikin dare, inda suka samu hotunan wasu mutane guda uku da ke tura keken daukar kaya a filin jiragen saman na Brussels, wanda ake zato su ne keda alhakin kai harin. Har yanzu dai ana kan neman daya daga cikin mutane ukun, mutumin da jaridun kasar ta Beljiyam suka bayyana da sunan Najim Laachraoui, wanda hukumomin kasar ke nema ruwa a jallo tun a makon da ya gabata.

Bayan harin birnin Paris da kuma afkuwar na Brussels wanda ake zargin suna da dangantaka, ana iya cewar hanyar tuntubar juna da ma bazuwar aiyyukan ta'addanci ya yadu fiye da yadda ake tsammani kenan? Guido Steinberg kwararre ne a kan yankin gabas ta tsakiya da aiyyukan tarzoma a cibiyar nazarin kimiyyar siyasa ta birnin Berlinna Jamu.

Mutanen da ake zargi da kai hari a Brussels
Mutanen da ake zargi da kai hari a BrusselsHoto: picture-alliance/dpa/Federal Police

"Hanyar tuntubar juna tsakanin 'yan ta'addan ya kara fadada fiye da yadda ya kasance a watan Nuwambar bara lokacin harin birnin Paris. Sanannen abu ne cewar akwai mutane da yawa da ke da hannu a harin na Paris amma mutum guda ne ya taimaka musu ta fannin sufuri. Amma yanzu ko shakka babu akwai mutane da yawa. Babban abin damuwa shi ne, ba mu san yawan mutanen da kuma wadanda ke shirye yadda za a kai irin wadannan hare-hare ba. Kuma akwai yiwuwar cewar, daya daga cikinsu yana da kimiyyar sarrafa bam. Wanda watakila ya samu horo a Kasar Siriya".

Wani babban jami'in Turai ya bayyana cewar akwai bukatar inganta hadaka wajen musayar bayanan sirri domin shawo kan batutuwan da suka jibanci tsanannin kishin addini da yakar ta'addanci. Ma'aikatar harkokin waje ta Tarayyar Jamus ta tabbatar da cewar akwai Jamusawa cikin mautane 270 da suka jikkata a hare-haren na Brussels.