1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Ci gaba da bincike a kan iyakoki

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 1, 2024

Jami'an 'yan sandan Jamus da ke gudanar da bincike na musamman a kan iyakokin kasar, sun gano kimanin mutane 2,448 da ke yunkurin shiga kasar ba bisa ka'ida ba.

https://p.dw.com/p/4lIWf
Jamus | 'Yan Sanda | Bincike | Kan Iyakoki
Rundunar 'yan sandan Jamus na ci gaba da kwakkwaran bincike a kan iyakokin kasarHoto: Revierfoto/Revierfoto

Rundunar 'yan sandan Jamus din ce ta sanar da haka, inda tace ta gano mutanen ne bayan da aka fadada bincike a kan iyakokin kasar a tsakiyar watan Satumbar da ya gabata. Rundunar ta bayyana cewa tsakanin 16 zuwa 30 ga watan na Satumba ta mayar da mutane 1,546, bayan da suka ketara kan iyakokin kasar ba bisa ka'ida ba. A cewarta an kuma kora wasu wasu 69 tare da haramta musu sake shiga, yayin da ta cafke wasu 49 da ake zargi da yin safarar mutanen.