Chutar Ebola tana ta'adi a Afirka ta Yamma
July 29, 2014Jami'an kiwon lafiya na kasar Saliyo sun bayyana cewa babban likitan kasar da ya kasance kan gaba wajen yaki da chutar Ebola, ya rasa ransa kwanaki kalilan bayan kamuwa da chutar ta Ebola.
Dr Sheik Umar Khan wanda ya taimaka wajen warkar da mutane fiye da 100 da suka kamu da chutar ta Ebola, ya kamu da chutar a wannan wata, inda kungiyar likitoci na gari na kowa, MSF, ta kula da shi a yankin arewacin kasar. Ana daukan Marigayi Dr Umar Khan a matsayin kwarzo na kasa, saboda yadda ya nuna jaruntaka wajen tunkarar chutar ta Ebola.
Kasar ta Saliyo ta kasance daya daga cikin kasashen yammacin Afirka da aka samu bullar chutar da Ebola mai saurin kisa. Kasashen yankin na yammacin Afirka na ci gaba da daukan matakan kariya.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu