1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masana sun gano yiwuwar annobar murar Aladu

Abdullahi Tanko Bala
June 30, 2020

Wani sabon bincike da aka gudanar a wasu gidajen kiwon Aladu a China ya gano yiwuwar barkewar annobar murar Aladu wadda tuni cutar ta kama wasu ma'aikatan gidajen gonar

https://p.dw.com/p/3ebJJ
China Afrikanische Schweinepest | Symbolbild Schweine in Shenzhen
Hoto: picture-alliance/imagechina/Y. Shuiling

Masu binciken kimiyya a China sun gano wani sabon nau'in cutar murar Aladu da za ta iya zama annoba a duniya kamar yadda binciken da aka wallafa a ranar Litinin da ta gabata a mujallar kimiyya ta Amirka ya nunar.

Sai dai wasu masana na cewa a yanzu cutar bata da wani hadari na gaggawa.

Kwayar cutar na yaduwa a tsakanin mutane kuma akwai bukatar sa ido sosai ko da za ta zama annoba a cewar wadanda suka wallafa binciken da suka hada da masana kimiyya daga jami'oin China da kuma cibiyar yaki da cutattuka masu yaduwa ta China.

Daga cikin kwayoyin cuttukan da masanan suka gano sun hada da nau'in G4 na kwayar cutar H1N1 wadda ke da dukkanin alamu na iya zama annoba.