1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China za ta taimaka wa ƙasashen Turai

February 15, 2012

Gwamnati a birnin Beijing ta jaddada cewar za ta ba da tallafi ga ƙasashen ƙungiyar Tarrayar Turai domin warwware matsalar kuɗi da ta addabi ƙasashen Turai.

https://p.dw.com/p/143Xd
BEIJING, Feb. 14, 2012 Chinese Premier Wen Jiabao (C), European Council President Herman Van Rompuy (L), and European Commission President Jose Manuel Barroso (R) meet with reporters after they attended the 14th China-EU summit at the Great Hall of the People in Beijing, capital of China, Feb. 14, 2012 pixel; picture alliance/ZUMA Press
Taron-China da-EUHoto: picture alliance/ZUMA Press

Wannan shawara  ta biyo bayan tattaunawar da aka soma tsakanin tawagogin ƙungiyar ta Eu  da kuma na ChinaTaron wanda aka gudanar  ya kasance na share fage ga taron ƙasashen China da na ƙungiyar Tarrayar Turai karo na 14 da za a gudanar nan gaba.Wanda tun can da farko aka so a gudanar da sauran wuri to amma matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita a nahiyar ta Turai ta sa aka ɗage shi har yazuwa cikin watan oktoba mai zuwa.Tura dai ta kai bango ga ƙashen na ƙungiyar Tarrayar Turai, waɗanda manyan hukumomin ƙiesta ƙimar ƙasshen duniya na biyan bashi na Moody's ta ƙara saka wasu ƙasashen Turan guda shidda cikin sahun ƙasashen da suka kasa, abinda ƙasar ta China ta ke ta ƙara yin nazari akan sa dangane da cewar nahiyar Turai ita ce nahiya ta farko da China  ta kan shigare da hajojinta.Da yake yin  sanarwa ba da haɗin kai ga nahiyar ta Turai a wajan taron domin  samar da mafita ga lamarin bashin da ya yiwa nahiyar ta Turai katutu fraministan China Wen Jiabao  ya ta tabatar da alƙawarin da ya yi.

China ta yi wa ƙasashen Turai alƙawari na agaza masu

ya ce fatan mu shi ne mu taimaka wa ƙungiyar Eu ta samar da masalha akan wannan rikici na kuɗi na ta da ya yi muni, ya ce muna da yardda da Turai da kuma Euro ya ce kuma China a shirye take ta yi aiki  da nahiyar Turai.Ko da shi ke wasu  manazarta na kallon cewar girma ya fadi kuma raƙumi ya shanye ruwan ya tsaki amma babu wani abin mamaki nahiyar ta Turai ta nemi agaji ga ƙasar da ke samin ci gaba akan sha'anin tattalin arziki na duniya wacce ke ta biyu.Kuma daman tun a kwanakin baya da suka wucce a ganawar da fraministan China ya yi da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel shugabannin biyu sun tattauna yi war ƙara ba da  gudun mowar da China ta ke bayar wa ga asusun ba da lamuni na IMF, wanda har yanzu China ba ta fayacce yawan kuɗaɗen da za ta bayar wa  ba.Shugaban majalisar ƙungiyar Tarrayar Turan Herman Van Rompuy ya yaba da yunƙurin da fraministan na China ya yi''ya ce muna jinjina wa alƙawarin da fraministan Wen Jiabao ya ɗauka domin samun sukunin tabbatar da ɗorewar darajar takardar kuɗin Euro''.

China's Premier Wen Jiabao (C) poses with European Council President Herman Van Rompuy (L) and European Commission President Jose Manuel Barroso after they met in the Great Hall of the People in Beijing February 14, 2012. China and the European Union began their summit meeting in Beijing today, after it was postponed from last December. It will bring together Premier Wen Jiabao and President Hu Jintao with European Commission President Jose Manuel Barroso and European Council President Herman Van Rompuy. Premier Wen said recently that China has a stake in helping Euro zone countries get through their debt crisis, adding that Beijing was considering increasing its participation in rescue funds to address the European debt crisis. REUTERS/David Gray (CHINA - Tags: POLITICS BUSINESS TPX IMAGES OF THE DAY)
Shugabannin ƙungiyar EU da na ChinaHoto: Reuters

China na buƙatar ƙasashen Turai su amince da matsayin ta na kasuwanci

Taron  ya sanar da cewar nan gaba za a buɗe shawarwari tsakanin  ƙasashen ƙungiyar Tarrayar Turan  da kuma China wacce ita ma ta ke buƙatar ƙasahen Turan da su amince da matsayin ta na kasuwanci kafin shekara ta 2016 abinda zai bai wa ƙasar China damar shiga kasuwannin Turai gadan gadan da kuma garanti. Daman a wani taron tattalin arziki da aka gudanar a cikin watan Satumba da ya gabata a Dalian shugaban gwamnatin na China ya gabatar da buƙatar ga ƙasashen Turan amma ba tare da samun nasara ba.Shugaban hukumar Tarrayar Turan Jose Manuel Borosso ya ce tilas ne su aiki tare da Chinan kafaɗa da kafaɗa.'ya ce a ɓangaren mu ƙarara ta ke  zamu yi duk abinda ya kamata mu yi domin ganin aminci da yarda sun  sake tabbata don cimma nasara akan abinda aka sama gaba.Za a iya cewar dai wannan hulɗa ta gaisuwa da neman iri za ta iya kasancewa ta bani gishiri na baka manda tsakanin ƙasashen biyu to amma kafin a kai ga gaci a yanzu nahiyar ta Turai ta cikin halin tsaka mai wuya na bashi da ya cin ƙarfin wasu ƙasashen har iya wuya.

EU President Herman Van Rompuy, center, receives a Chinese calligraphy work as a gift from psychiatric patients during his visit at an EU-funded psychiatric clinic in Beijing Tuesday, Feb. 14, 2012. (Foto:Alexander F. Yuan/AP/dapd)
Herman Van Rompuy Shugaban majalisar ƙungiyar Trrayar TuraiHoto: AP

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita        : Umaru Aliyu