1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar corona na barazana a China

Binta Aliyu Zurmi
November 15, 2021

Kasar China na fuskantar barazana mafi girma ta sake barkewar sabon na'uin Covid-19 na Delta mai saurin yaduwa

https://p.dw.com/p/42zc5
China WHO Corona-Ursprung
Hoto: Xiong Qi/XinHua/dpa/picture alliance

Sama da mutum 1,300 aka sanar da sun kamu da na'uin cutar ta Delta a kasar daga tsakiyar watan Oktoba zuwa Nuwamba, lamarin da ya zarce adadin da aka samu a kasar a lokacin rani.

Yanzu haka dai kasar ta China na zama a sahun gaba da yawan masu dauke da wannan sabon na'uin na corona wato Delta. Kuma mahukunta sun tabbatar da bazuwar nau'in na Delta zuwa lardunan kasar 21 gami da wasu yankuna.

Tuni ma wasu yankuna suka fara hana al'ummar da suka fito daga yankin da cutar ta yi kamari shiga inda suke.

A ranar Lahadi kadai China ta sami sama da mutum 88,000 sabbin kamuwa da corona yayin da sama da mutum 4,5000 suka rasa rayukansu.

Cutar corona da ta samo asali daga kasar ta China a karshen shekarar 2019 har yanzu ta na ci gaba da yaduwa a sassa daban-daban a duniya.