1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

China: Sarrafa makamin nukiliya domin kare kai

June 12, 2022

Mahukunta a Chinan sun ce za su yi amfani da makamin nukiliyar ne kawai a wurin kare kansu, kuma ba za su taba fara amfani da makamin ba, sai idan wani ya fara kawo musu hari da shi.

https://p.dw.com/p/4Ca9s
BG Nuklearwaffen | chinesische Dongfeng-41 Raketen
Hoto: Zhang Haofu/Xinhua/picture alliance

China ta yi nisa wurin kera makaman nukiliya. Ministan tsaron kasar Wei Fenghe ne ya sanar da haka a wannan Lahadi a yayin taron koli kan harkokin tsaron yankin Asiya da ke gudana a Singapore. Ministan ya ce shekaru sama da 50 suka kwashe suna kokarin kera makamin.


Tun a shekarar da ta gabata Amirka ta ce ta bankado yadda China ke bunkasa makamashin nukiliya ba tare da sanin duniya ba. To sai dai ministan tsaron Chinan ya ce burin kasarsa shi ne kokari na dakatar da amfani da makamin kare dangi a duniya ta hanyar kare martabarta.