1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kai ruwa rana tsakanin China da Taiwan

Abdourahamane Hassane
December 26, 2022

Taiwan ta ce sojojin kasar China sun sake keta sararin samaniyarta. A cewar ma'aikatar tsaro a birnin Taipei, jiragen saman kasar China 71 da jiragen ruwa bakwai sun kasance a kusa da Taiwan cikin sa'o'i 24.

https://p.dw.com/p/4LQvQ
Indien, Uttarakhand | Indisch - US-Amerikanische Militärübung Yudh Abhyas
Hoto: Manish Swarup/AP/picture alliance

Jami'ai sun ce Jirage 47  suka tsallaka tsakiyar mashigin tekun Taiwan. Mashigin ya raba yankin Taiwan mai mulkin dimokuradiyya da China. China ta ce ta yi atisayin sojojin ne a cikin teku da sararin samaniya tsibirin, domin mayar da martanin a game da matakin da Amirka ta dauka a baya-baya nan. Inda Majalisar dokokin Amirkan ta zartas da sabon kasafin kudin gwamnati a ranar Juma'a, wanda ya hada da sabbin lamuni ga Taiwan domin sayen makamai.