1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

China ta yanke wa wasu 'yan Uyghur hukuncin kisa

April 7, 2021

Mahukunta a lardin Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar China sun yanke hukuncin kisa ga wasu tsoffin jami'an gwamnati 'yan kabilar Uyghur biyu da ke yankin.

https://p.dw.com/p/3rgMq
Tableau | Xinjiang - Baumwollanbau | Uighren | 25.03.2021
Hoto: Kevin Frayer/Getty Images

An dai yankewa jami'an Musulmai hukuncin da za a jinkirta aiwatar wa na tsawon shekaru biyu bisa laifin yunkurin ballewa da ma amsar cin hanci da rashawa.

An tuhumi Shirzat Bawudun tsohon shugaban sashin shari'a na yankin da aikata laifin baiyana asirin kasa da kuma hannu cikin wasu ayyukan ta'addanci na kungiyar ETIM.

Shi kuwa tsohon daractan illimin yankin Sattar Sawut an tuhume shi ne da sanya batutuwan da suka shafuka na tsattsaurar ra'ayin addini da rikice-rikice da kuma ballewa cikin litattafan makarantun yankin wanda kotu ta alakanta hakan da harin da aka kai babban birnin yankin Urumqi a shekarar 2009 ya kuma yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin dari 2.

Gwamnatin China dai ta ce ta na ci gaba da zakulo jami'an gwamnati da ke da fuska biyu kuma suke yin zangon kasa ga mulkinta a yankin, sai dai har kawo yanzu ana zargin gwamnatin kasar da take hakkin bil adama a yankin.