1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta tsananta matakan bawa 'yan jaridun ƙetare izinin aiki a cikin ƙasar

March 6, 2011

An soki lamirin hukumomin China game da muzguna wa 'yan jarida na ƙetare a ƙasar, a wani mataki na hana watsa labarun zanga zangar ƙin jinin gwamnati.

https://p.dw.com/p/10UHY
Jami'an tsaron China na kawo wa 'yan jaridar ƙetare ciƙasHoto: dapd

Bayan kiraye kirayen gudanar da zanga-zangar ƙyamar gwamnatin China, hukumomin ƙasar sun tsananta dokokin bawa 'yan jaridar ƙetare izinin aiki a cikin ƙasar. Wani kakakin ma'aikatar harkokin ƙetare a birnin Beijing ya sanar cewa dole masu aiko da rahotannin sun nemi izini na musamman ga kowane irin labarin da za su watsa. A birnin Shanghai an kama 'yan jarida na ƙasashen ƙetare da dama ciki har da wakilin mujallar Stern ta Jamus a China. Da farko an kira zanga zangar nuna ƙin jinin gwamnati a birnin mai tashar jiragen ruwa. A halin da ake ciki gwamnatin China ta ba da sanarwar ɗaukar matakan magance matsalar hauhawar farashin kaya.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a wannan Lahadin ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya soki China bisa matakan tsare 'yan jarida na ƙetare, yana mai cewa matakan gwamnati na kawo ciƙas ga aikin jarida ba abin karɓuwa ba ne. Wannan sanarwar ta biyo bayan rahotannin dake nuna cewa China ta kame 'yan jarida da dama daga ƙetare. Westerwelle ya ce wannan labari ne mai damuwa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita; Umaru Aliyu