1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta rinɓanya agajin da ta ke bai wa ƙasashen Afirka

July 19, 2012

Taron ,China da ƙasashen nahiyar Afirka na tattaunawa kan ƙara ƙarfafa hulɗa tsakanin ƙasashen

https://p.dw.com/p/15b1J
Source News Feed: EMEA Picture Service ,Germany Picture Service China's President Hu Jintao delivers a speech during the opening ceremony of the Fifth Ministerial Conference of the Forum on China-Africa Cooperation (FOCAC) at the Great Hall of the People in Beijing, July 19, 2012. Hu on Thursday offered $20 billion in loans to African countries over the next three years, boosting a relationship that has been criticised by the West and given Beijing growing access to the resource-rich continent. REUTERS/Jason Lee (CHINA - Tags: POLITICS BUSINESS)
Hoto: Reuters

Kasar China ta sanar da riɓanya kuɗaɗen agaji na bashi da ta ke bai wa nahiar Afirka, wanda yawan su ya kai biliyan dubu 20.Shugaba Hu Jintao na Chinar shi ne ya sanar da haka a gaban shugabannin ƙasahen nahiyar ta Afirka ,a taron China da ƙasahen nahiyar Afirka karo na biyar da ke gudana a birnin Bejin.

Tun a shekara ta 2009 China ta kasance abokiyar hulda ta farko ta nahiyar Afirka,wanda kuma kawo yanzu yawan agaji da take bai wa nahiyar ya kai kashi 60 cikin ɗari na agajin da ta fitar wa zuwa ƙasashen waje.A na sara a ƙarshen taron shugabannin ƙasahen zasu cimma ƙarin yarjejeniyoyi na cinikkaya tsakanin China da ƙasashen nahiyar Afirka.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman