1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta musunta mutuwar Jiang Zemin

July 7, 2011

Gwamnatin China ta musunta raɗi-radin dake nuni da mutuwar tsohon shugaban ƙasar, Jiang Zemin tare da hana neman bayani akansa ta yanar gizo

https://p.dw.com/p/11rAt
Taswrar kasar China

Ƙasar China ta ƙaryata jita-jitar cewa tsohon shugabanta, Jiang Zemin ya mutu. An dai sha yayata raɗi-radin cewa tsohon shugaban yana fama da rashin lafiya sakamakon ganin shi da ba a yi ba gun bukin cika shekaru 90 na kafuwar jam'iyyar kwaminisanci da ke mulkin ƙasar da ya gudana a ranar Juma'ar da ta gabata. Kamfanin dillacin labaru na gwamnatin China ya musunta mutuwar Jiang amma ba tare da yin ƙarin bayani game da lafiyarsa ko kuma inda yake ba. Masu kula da aikin watsa labarai na ƙasar ta China sun toshe hanyonin neman sunan Jiag ko kuma duk wani abu da ya dangance shi a shafukan yanar gizo tare da yin kashedin cewa yin hakan babban laifi ne.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita. Ahmad Tijani Lawal