1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta gargadi Kanada kan Hong Kong

Zulaiha Abubakar
August 19, 2019

Ofishin jakadancin kasar China a Kanada ya gargadi kasar ta kiyayi sanya baki a harkokin cikin gidan yankin Hong Kong, kwana guda bayan China ta kare kanta daga zargin take hakki.

https://p.dw.com/p/3O6Rr
Hongkong Protest gegen China & Auslieferungsgesetz
Hoto: Getty Images/AFP/I. Lawrence

Gabanin wannan kare kai daga gwamnatin China, an jiyo ministar harkokin kasashen wajen kasar Kanada Chyrstia Freeland da shugabar manufofin harkokin wajen kungiyar EU Federica Mogherini suna jaddada muhimmancin 'yancin fadin albarkarcin baki da kuma zanga-zangar lumana a matsayin wajibi bayan sun bayyana takaici game da yadda rikici ke kara kamari a Hong Kong.

Masu zanga-zangar dai sun ci alwashin cigaba da kyamar gwamnatin yankin har ta amince da bukatunsu, duk kuwa da irin kiraye-kirayen sulhun da kasashe ke yi wa bangarorin biyu.