1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta caccaki Amirka kan batun Hong Kong

Binta Aliyu Zurmi
May 29, 2020

China ta yi tir da matakin Amirka a kan dokar tsaro ta yankin Hong Kong, ta kuma yi kira ga kasashen duniya da su janye bakinsu a harkokinta na cikin gida kana su guji jan ra'ayin Majalisa Dinkin Duniya kan batu.

https://p.dw.com/p/3cyHA
China Nationaler Volkskongress | Sicherheitsgesetz Hongkong | Xi Jinping, Präsident
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Schiefelbein

China dai ta dade tana kiran kasashen duniya da su daina tsoma mata baki a harkokinta na cikin gida, amma hakan bai hana kasashe irinsu Birtaniya da Kanada da Ostireliya da ma Amirkan sukar matakinta na bijiro da sabuwar dokar da ta yi sauyi ga tsarin tsaro a yankin Hong Kong din.

A jiya Alhamis ce majalisar dokokin kasar China din ta amince da dokar ta yankin Hong Kong mai sarkakiya, matakin kuma da ake ganin zai bude wani sabon babi na rikici a yankin.