1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China: Fatali da dokar kare masu boren Hong Kong

Abdoulaye Mamane Amadou
November 21, 2019

China ta sha alwashin mayar da martani da kakkausan lafazi ga Amirka, biyo bayan amincewar da majalisar dokokin kasar ta yi da wasu kudurorin doka da ke kare hakin masu rajin girka dimukuradiyya a yankin Hong Kong.

https://p.dw.com/p/3TT3u
Hongkong - USA | Versammlung zum Menschenrechts- und Demokratiegesetz
Hoto: picture-alliance/ZUMAPRESS.com/K. Tsuji

A wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen China Wang Yi, ya caccaki matakin na majalisar dokokin Amirka, yana mai bayyana shi a matsayin wata mumunan alama ga masu boren yankin da ya kira da bata gari, kana kuma matakin ka iya zama illa da ma tarwatsewar yankin na Hong Kong.

Wannan matakin na zuwa ne a yayin da har yanzu wasu kwarorin masu bore ke markaye a cikin jami'ar yankin, inda suke suka kwashe tsawon kwanaki suna artabu da jami'an tsaro, a yunkurin hukumomin 'yan sanda na ganin sun bayar da kansu.