1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China na son a warware rikicin Ukraine

Ahmed Salisu
April 7, 2023

Shugaban China Xi Jinping ya bayyana a wannan Juma'ar cewar amfani da hanyoyi na siyasa ne kadai mafita wajen kawo karshen yakin da Rasha ke yi a kasar Ukraine.

https://p.dw.com/p/4PpH3
Ukraine Krieg | Ukrainische Soldaten bei Kreminna
Hoto: Roman Chop/AP/picture alliance

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen China ta fidda ta rawaito shugaban na China na cewar ya kyautu bangarorin biyu da ke kai ruwa rana da juna su hau teburin tattaunawa don kawo karshen rikicin da ke wakana tsakaninsu.

Shugaban na China dai a baya-bayan nan na kokari wajen ganin manyan kasashen duniya da ke rikici da juna sun mayar da wukakensu cikin kube, don ko a 'yan kwanakin da suka gabata ya shiga tsakanin Iran da Saudiyya wanda hakan ya sa suka fara shirin maido da huldar diflomasiyya tsakaninsu.