1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina ta mayar wa da Amirka martani

Gazali Abdou Tasawa MNA
August 8, 2018

Chaina ta sanar a wannan Laraba da shirin dora karin kaso 25 daga cikin 100 na haraji kan wasu hajojin kasar Amirka da ake shiga da su a kasarta.

https://p.dw.com/p/32rEp
Südafrika | Xi Jinping spricht auf dem BRICS Summit
Hoto: picture-alliance/dpa/Xinhua News Agency/L. Xueren

Kasar Chaina ta sanar da shirin dora karin kaso 25 daga cikin 100 na haraji kan hajojin kasar Amirka da ake shiga da su a Chainar. Wannan kuwa a matsayin martani ga matakin da Amirka ta dauka a ranar shida ga watan Yulin da ya gabata wanda ya tanadi karin harajin da ya kai na miliyan dubu 50 kan hajojin kasar ta Chaina. 

Wannan dai shi ne karo na farko tun bayan takun sakar harkokin kasuwancin da ya hada kasashen biyu da kasar Chainar ke daukar irin wannan mataki kan kasar ta Amirka. 

A wani sako da ofishin ministan kudi na Chaina ya wallafa a shafinsa na yanar gizo, ya ce sabbin matakan harajin da kasar ta Chaina ta dauka kan kasar ta Amirka da kuma ta ce za su soma aiki daga ranar 23 ga wannan wata na Agusta, za su shafi kayayyaki kamar su ma'adanin kwal da wasu na'urori na aikin likita ko kuma na sarrafa shara.