1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chen Guancheng ya tsere daga gidansa

April 27, 2012

Dan gwagwarmayar kare hakkin bil Adama a China ya nemi mafaka a birnin Beijing

https://p.dw.com/p/14mDi
FILE - In this Jan. 2011 image made from video released on Feb. 10, 2011, by China Aid Association, Chinese activist and lawyer Chen Guangcheng speaks in Dongshigu village, Shandong province, China. A blind Chinese activist, Chen Guangcheng, under house arrest was beaten into unconsciousness by local authorities and denied medical care, his wife said in a handwritten letter that was smuggled out of the couple's tightly guarded home. (Foto:China Aid Association/AP/dapd).
Chen GuangchengHoto: AP

A kasar China fitaccen dan rajin kare hakkin bil Adaman nan, Chen Guancheng ya tsere daga daurin talalar da ake masa a gidansa. Danginsa da kungiyoyin kare hakkin bil Adama na kasa da kasa sun ce Chen wanda makaho ne mai shekaru 40 ya tsere ne wa jami'an da ke tsare da shi ne a kauyen Dongshigu da ke lardin Shandong na gabashin kasar. Kungiyar kasar ta China da ke gudun hijira a Amirka, wato ChinaAid ta ba da rahoton da ke nuni da cewa ya nemi mafaka a birnin Beijing. Shi dai Chen yana gwagwarmaya ne domin kau da manufar tilasta zubar da ciki da kuma juya mahaifa a kasar ta China. An ci gaba da tsare shi a gidansa ne bayan da ya cika rabin wa'adin hukuncin daurin da aka yanke masa a gidan kaso a watan Satumban shekarar 2010.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu