1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murna ta koma ciki kan yaki da corona

Zulaiha Abubakar
June 25, 2020

Ma'aikatar Lafiya ta Chaina ta tabbatar da cewar mutane 19 sun kamu da cutar coronavirus yayin da hukumomi suka dauki sabbin matakan yaki da cutar bayan sake bullar ta a birnin Beijing.

https://p.dw.com/p/3eIuY
China Peking | Coronavirus | Testzentrum
Hoto: Reuters/C.G. Rawlins

Jimillar wadanda suka kamu a wannan lokaci da annobar ta coronavirus da sake yin kome a Chaina ya kai 269 to sai dai jami'an lafiya sun danganta hada-hadar jama'a a wata kasuwa dake Kudu maso yammacin yankin Fentai da cewar ita ce ta haifar da yaduwar cutar cikin kankanin lokaci.

Yanzu haka dai hukumomi sun dauki tsauraran matakan dakile cutar a yankunan da ta sake bulla ta hanyar kaddamar da sabon gwaji da rufe makarantu da sabuwar dokar kulle da kuma haramta tafiye-tafiye wadanda basu zama wajibi ba.