1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan rajin kare hakkin bil'adam zai fuskanci dauri

Zulaiha Abubakar
July 29, 2019

Wata kotu a kasar Chaina ta yankewa Huang Qi dan rajin kare hakkin bil'Adama hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 20 bayan samunsa da mallakar manhajar tattara bayanan cin zarafi a Internet .

https://p.dw.com/p/3Mvh4
China Huang Qi
Hoto: Getty Images/AFP/F. Dufour

Huang mai shekaru Hamsin na zaman kaso a gidan yarin kasar tun shekara ta 2016 bayan sanya masa takunkumin siyasa har na tsawon shekaru hudu, almarin da Majalisar Dinkin Duniya da wasu kungiyoyin hakkin 'dan Adam  da kuma mahaifiyarsa suka bayyana rashin jin dadinsu a kai.

Kafin tsare shi 'dan gwagwarmaryar ya yi fice a fagen nemarwa wadanda aka raba da muhallansu hakkinsu, ciki har da mutanen da girgizar kasa ta shafi muhallansu a Kudu masi Yammacin yankin Sichuan tun shekarar ta 2008 .