1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChadi

Faransa na zargin shugaban kasar Chadi

July 3, 2024

Kasa da watanni biyu bayan shan rantsuwar kama mulki, shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby Itno na fuskantar tuhuma daga hukumomin shari'ar Faransa.

https://p.dw.com/p/4hpy6
Chadi | Shugaban Kasa | Mahamat Idriss Deby Itno | Zargi | Faransa
Zababben shugaban ksar Chadi Mahamat Idriss Deby ItnoHoto: Israel Matene/REUTERS

Faransan dai na zargin zababben shugaban kasar na Chadi Mahamat Idriss Deby Itno da wadaka da dukiyar jama'a, tare da boye kadarori da kuma yin almubazzaranci wajen sayen suturu na alfarma. Kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa tuni babban Ofishin Yaki da Cin-hanci da Rashawa na kasar Faransa da ake wa lakabi da OCRGDF ya fara bincikar Shugaba Deby kan wadannan zarge-zarge ne, tun a farkon watan Janairun da ya wannana shekara bayan da wata mujalla da ake wa lakabi da Mediapart ta wallafa rahoto a cikin watan Disambar bara.

Karin Bayani: Shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby Itno ya nada sabon firaminista

Mujallar ta ruwaito cewa Shugaba Deby da ya hau kan madafun ikon Chadi bayan rasuwar mahaifinsa ya kashe zunzurutun kudi da ya kai Euro dubu 900 wajen sayen suturu na alfarma, ta hanyar wani kamfani da ke kasar ta Chadi da ya biya makudan kudin a wani banki. Wannan lamari ya firgita 'yan Chadi, la'akari da halin kunci da talauci da tallakawan kasar da ke gabashin Afirka ke ciki a karkashin mulkin iyalan Deby. A cewar dan fafutuka Andre Ngombe Melewa wannan badakala na nuni karara da cewa, Deby ya bi sawun shugabannin kama-karya na wasu kasashen Afirka  da ke boye kudin sata a kasashen ketarte.

Chadi | Adawa | Succes Masra
Tsohon firaministan Chadi kana jagoran adawa Succes MasraHoto: Issouf Sanogo/AFP

Dama dai a cewar dan adawa Max Kamkoye wannan lamari ba bakon abu ne ba a Chadi, domin kasar ta kwashe shekaru sama da 30 karkashin shugabanni da mukarrabansu masu ci-da-gumin tallakawa ba tare da sun fuskanci shari'a ba. To sai dai magoya bayan shugaba Deby wanda ya lashe zaben Chadi da gagarumin rinjaye tun a zagayen farko a watan Mayun da ya gabata kamar Hadiza Mouhammed Ibrahim mazauniyar birnin N'Djamena na da ra'ayin cewa, kashin kaji kawai ake so a gogawa shugaban ta hanyar wadannan zarge-zarge.

Karin Bayani: Gwamnatin farar hula ko ta soja a Chadi?

A can baya dai Shugaba Mahamatt Idriss Deby ya yi watsi da wadannan zarge-zarge, cikin wani littafi da ya wallafa gabanin zabensa. To amma tun bayan sake bankado da badakalar, shugaban da makusantansa sun ki cewa uffan game da batun da tuni ya fara tayar da kura a kasar ta Chadi. Ana dai sa ran wannan bincike ya fadada zuwa kadarorin da iyalan Deby suka mallaka a kasar Faransan, tun daga lokacin mulkin mahaifinsa zuwa yanzu.