1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi ta yi afuwa ga daruruwan 'yan tawaye

November 29, 2021

Majalisar soji a Chadi ta sanar da yin afuwa ga kimanin 'yan tawaye 300 a wani mataki na amincewa da bukatun kungiyoyin adawar da gwamnatin kasar ta yi.

https://p.dw.com/p/43dZJ
Tschad | Mahamat Idriss Déby, Präsident des Übergangs-Militärrates (CMT)
Hoto: Brahim Adji/Tchad Presidential Palace/AFP

Majalisar ministocin kasar ta ce afuwar za ta shafi wadanda aka yanke wa hukunci kan laifukan ta'addanci da zubar da martabar kasa da kuma laifukan da suka shafi baiyana ra'ayi na kashin kai. 

Kungiyoyin 'yan tawayen kasar dai sun ce yin afuwar na daga cikin sharuddan da suka kafa kafin zama kan teburin tattaunawa da shugaban kasar Mahamat Idriss Deby Itno, wanda ya maye gubin mahaifinsa da aka kashe a watan Afrilu.

Tun dai bayan hawa kan karagar mulkin kasar, Mahamat ya rusa majalisar dokokin kasar tare da soke kundin tsarin mulki, inda ya yi alkawarin gudanar da zabe cikin adalci a cikin watannin 18.