1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi: An kafa gwamnatin hadin kan kasa

Ahmed Salisu RGB
October 17, 2022

A kokarinsu na ganin sun daidaita al'amura a kasar Chadi, mahukuntan kasar sun girka gwamnatin hadin kan kasa karkashin jagoranci fitattacen dan adawa Saleh Kebzabo.

https://p.dw.com/p/4IISV
Fadar gwamnatin Chadi
Firaiminista Saleh Kebzabo a fadar gwamnatiHoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft der Republik Tschad

A kokarinsu na ganin sun daidaita al'amura a kasar Chadi, mahukuntan kasar sun girka gwamnatin hadin kan kasa karkashin jagoranci fitattacen dan adawa Saleh Kebzabo. Sabuwar gwamnatin ta kunshi tsofaffin 'yan tawaye wanda ke ciki da wajen kasar. Sabon firaministan ya sha alwashin ganin an hade kasar waje guda tare da tabbatar da kawar da tarin matsalolin da ke gabanta. 

Firaministan Saleh Kebzabo ya ce, shi da ministocinsa sun dukufa wajen ganin sun fidda kasar ta Chadi daga cikin dumbin matsalolin da ta samu kanta a ciki kuma babban abin da suka mayar da hankali a yanzu shi ne, hade kan 'yan kasar waje guda musamman idan aka yi la'akari da irin rarrabuwar kawuna da ake da su wanda suka taimaka wajen haifar da matsalolin da suke fuskanta duk kuwa da cewar wasu 'yan tawaye sun kaurecewa shiga gwamnati da shirin gwamnatin na samar da zaman lafiya.

Chadi | Mahamat Idriss Deby
Mahamat Idriss DebyHoto: Aurelie Bazzara-Kibangula/AFP/Getty Images

Baya ga batu na hade kan 'yan kasar wanda firaminista ke cewar shi ne danba na wanzar da zaman lafiya, ya ce gwamatinsa ta fara aiki tukuru wajen kawar da matsalolin da ake samu a tsakanin manoma da makiyaya wadda a cewarsa matsala ce babba.

''Abin da muka sanya a gaba shi ne, hadin kan kasa don kasarmu na cikin yanayi na tashin hankali da rarrabuwar kai. Dole ne mu yi yaki da wadannan matsaloli wanda akasarinsu rikici ne tsakanin manoma da makiyaya.''

Idriss Deby Itno
Marigayi Idriss Deby ItnoHoto: Blaise Dariustone/DW

Koma baya na tattalin arziki ma dai na daga cikin irin kalubalen da Chadin ke fuskanta, kuma firaministan kasar ya ce, za su tinkari matsalar gadan-gadan, inda a share guda ya yi wa 'yan kasar alkawarin yin gyara a fannin shari'a da kuma tallafawa wadanda ambaliya ta yi wa ta'adi a baya-bayan nan.

''Kasarmu na fuskantar matsalolin da suka danganci tattalin arziki da matsaloli nan da can a fannin shari'a na kasar. Burinmu shi ne mu yi maganin wadannan matsaloli. Baya kuma ga wadannan matsaloli, muna fama da matsalar ambaliya wadda ta yi ta'adin da zai dau lokaci da makudan kudade wajen gyara. Wannan shi ne kalubalen da ke gabanmu da muke fatan ganin mun kawar.''

Yanzu haka dai 'yan kasar ta Chadi na zuba idanu don ganin kamun ludayin sabuwar gwamnatin da irin sauyin da za ta samar a tsukin shekaru biyu da za ta shafe tana mulki kafin a kai ga yin zaben da zai haifar da sabuwar gwamati ta farar hula a kasar.