1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar kin jinin gwamnatin mulkin soja a Chadi

Abdoulaye Mamane Amadou
May 8, 2021

'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla wajen tarwatsa kwarorin masu rajin dawo da tsarin dimukuradiya a kasar Chadi wanda rukunin 'yan adawa ya kira.

https://p.dw.com/p/3t8pF
Tschad N'Djamena | Proteste und Gewalt
Hoto: ISSOUF SANOGO/AFP

A wannan Asabar ne 'yan sanda cikin shirin ko takwana suka tarwatsa masu gangamin kinjinin gwamnatin mulkin soja a Chadi, wacce ke karkashin jagorancin dan tsohon shugaban kasar mariganyi Idris Daby Ito wato Mahamat Idriss Déby.

Shedun gani da ido sun ce wasu kwarorin mutane sun fito a unguwanni na biyar da na shida da ke binrin N'Djamena, tare da yin kone-konen tayoyi ciki har da kona tutar Faransa, kasar da masu boren ke zargi da marawa sabon shugaban kasar Chadin baya, sai dai ba a jima ba 'yan sanda suka tarwatsa gungun matasan.

Daman dai tun a wannan Juama'a hukumomin kasar suka fitar da sanarwar haramta zanga-zangar, bisa abinda suka kira rashin cika sharuda.