1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi: Lauyoyi za su kaurace wa zaman kotu

Mouhamadou Awal Balarabe
June 10, 2018

Lauyoyin Chadi sun sha alwashin ci gaba da yajin aiki tare da kaurace wa zaman kotu na mako guda matukar ba a tsige wadanda suke da hannu wajen cin zarafin abokin aikinsu ba.

https://p.dw.com/p/2zEog
Tschad Mahamat Hassan Abakar
Hoto: DW/B. Dariustone

Lauyoyi na kasar Chadi da sauran jami'an da ke aikin kare dokoki sun yanke shawarar ci gaba da yajin aikin har i zuwa akalla 13 ga watan Yuni, duk da karamcin da gwamnatin ta yi na korar gwamnan yankin kudu da ake zargi da cin zarafin wani lauya da kuma wasu da yake karewa. Babban burinsu a yanzu dai shi ne ganin cewa an kori sojoji da kuma manyan jami'ai da ke da hannu a wannan rikici, a cewar babban sakataren kungiyar lauyoyin Chadi Djimadoun Koumtog .

A ranar 22 ga watan Mayu ne wani lauya da ke aiki a Doba da ke kudancin kasar ya ce Jandarmomi sun harbi motarsa yayin da yake jigilar wadanda yake karewa bayan da kotu ta sallamesu. Kwamitin bincike da aka kafa daga bisani ya bada shawarar sallamar gwamnan Doba da kuma kwamandan na Jandarma daga bakin aiki.  Sai dai duk da haka lauyoyi suka ce za su shirya zanga-zangar lumana a ranar 16 ga watan Yuni a babban birnin kasar Chadi Ndjamena tare da kauracewa wa zaman kotu a ranar 11 ga watan Yuni zuwa 20 don nuna fushinsu.