1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi na son koyon dabarun mulki daga Mali

Abdoulaye Mamane Amadou
August 6, 2021

Matakin gwammnatin rikon kwaryar Chadi na tura wata tawagar koli zuwa kasar Mali don koyo salon yadda gwammnatin kasar ke tafiyar da mulkinta na rikon kwarya ya bar baya da kura.

https://p.dw.com/p/3yep3
Mali Treffen Assimi Goïta Delegation Tschad
Hoto: Mali Presidency

Tawagar kolin karkashin jagorancin Jean Bernard Padaré, tsohon minista kuma babban sakataren jam'iyyar MPS ta tsohon shugaban Chadi Idriss Daby ta shafe tsawon kwanaki biyar a Mali tana tattauna wa da bangarori dabam-dabam a wani yunkuri na koyon yadda Mali ta kafa majalisar mulkin soja da kuma yadda harkokin mulkinta ke tafiya. A wata hira da DW kakakin tawagar Jean Bernard Padaré, ya ce ziyararsu a babban birnin Bamanko ta yi armashi.
 

"Ya ce mun tattauna da hukumomin Mali kan batutuwa da dama daga ciki har da yadda suka tsara dauka da nada manyan mukamai da yadda suka tattara takardun jama'a har aka kai ga tantance wadanda suka nadan. Mun kuma gana da shugaban rikon kwarya Assimi Goïta inda ya bamu muhimman shawarwari tare da jan hankali kan saka kishin kasa ga duk matakan da muke shirin dauka a gaba."
Sai dai ziyarar tawagar a Mali ta bar baya da kura inda a Chadi dubban magoya bayan kungiyoyin farar hulla suka soki lamirin tawagar suna masu cewa Mali bata yi kimar da take iya koyar da Chadi wani yanayin mulki ba a cikin wannan tafiyar.  Alain Kemba Didah shi ne jagoran kungiyoyin fararen hula masu rajin girka Dimukuradiyya na Wakittamma a Chadi.

Mali Premierminister Mali Choguel Kokalla Maïga
Hoto: Mahamadou Kane/DW

"Ya ce muna ganin babban abin yi shi ne majalisar soja ta wucin gadi kamata yayi ta kira taron koli na tattaunawa kan al'amurran kasa wato Conference Nationale, to amma sai dai har yanzu muna ganin gwamnatin na nuna turjiya kan wannan batu. A gremu babban abin kunya ne a ce wai kasa kamar Chadi ta nemi wata shawarar yadda za ta tafiyar da mulki ga wata kasar da ita kankanta neman kanta take."

Mali Premierminister Mali Choguel Kokalla Maïga
Hoto: Mahamadou Kane/DW

Shi ma dai Moussa Sidibe mai sharhi kan harkokin siyasar mali cewa ya yi bai ga dalilin da zai sa Mali ta koyar da Chadi ba saboda ita kanta tana fama da kura-kuran da bai dace Chadin ta yi koyi da su ba.

" Ya ce ba na tsammanin majalisar rikon kwarya a Mali ta zama wata abar misali ga Chadi, domin kuwa ko ba komai basu mutunta tsarin tafiyar da gwamnbatin ba, wannan wata katobara ce kawai domin Mali ba za ta taba zama abar misali ba a yanzu kan tafiyar da yanayin mulkin rikon kwarya."

Ko baya ga Mali rahotanni na cewar akwai yiwuwar tawagar ta kara yada zango a Sudan a wani yunkuri na daukar salon mulki na gwmanatin rikon kwarya.