1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon harin Boko Haram a Chadi

Zainab Mohammed Abubakar
March 22, 2019

Harin dai ya auku ne a garin Dangdala, inda mayakan suka yi awon gaba da kayayyaki da na'urorin Sojojin

https://p.dw.com/p/3FVNT
Soldaten aus dem Tschad Archiv 2014
Hoto: AFP/Getty Images/M. Medina

Sojoji 23 aka kashe a yankin Kudu maso Yammacin kasar Chadi a wannan Juma'ar, a wani hari da mayakan Boko Haram suka kai musu, a cewar majiyar dakarun a birnin N'Djamena.

A ta bakin jami'in sojin kasar, mayakan na Boko Haram sun afkawa sansanin dakarun na Chadi da misalin karfe daya na dare, inda suka kashe 23 daga cikinsu.