1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fadan manoma da makiyaya ya hallaka jama'a a kasar Chadi

Abdoulaye Mamane Amadou
August 9, 2019

Hukumomi a Kasar Chadi sun tabbatar da mutuwar mutane 37 sakamakon wani rikicin da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a wani lardin da ke gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/3NekT
Tschad Präsident Idriss Deby Itno
Hoto: Getty Images/AFP/J. Demarthon

Da yake magana da manema labarai a birnin N'Djamena, Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno ya bayyana rikicin kabilanci da na manoma da makiyaya da zaman wani babban bala'in da ke addabar kasar a yanzu, inda ya ci gaba da cewa masu rikicin sun yi ta bude wuta ga jami'an tsaron da aka tura a lardin don kwantar da tarzoma a lardin Ouaddai da ke gabashin kasar Chadi.