1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama kan yi wa jagoran Boko Haram afuwa

Ramatu Garba Baba
February 26, 2022

Cece-kuce ya biyo bayan matakin da Shugaba Bazoum na Nijar ya dauka na yi wa wasu mayakan Boko Haram afuwa. Ya kare matakin da yunkurin samar da tsaro.

https://p.dw.com/p/47eu4
Deutschland l Besuch des Nigerianischen Präsidenten in Berlin
Hoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

Ana ci gaba da cece-kuce kan matakin da gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dauka na yin afuwa ga wasu mayakan Kungiyar Boko Haram da ke tsare a wasu gidajen yarin kasar, daga cikin wadanda aka yi ma afuwan, har da daya daga cikin jagororin kungiyar da ke tsare a wani gidan yarin kasar mai makwabtaka da Najeriya, inda Kungiyar Boko Haram ta samo asali.

Shugaba Mohamed Bazoum ya sanar da shirin yin afuwan, a lokacin wani taro da yayi da wasu manyan 'yan siyasa da shugabanin kungiyoyin farar hula da malamai dama sarakunan gargiya a Juma'ar da ta gabata, a taron shugaban ya kuma tabbatar da hikiman neman taimakon sojojin Takuba na Turai, daga bisani ya gabatar da hujjojin da suka saka shi amincewa da sojojin na Takuba, da ya ce, da taimakonsu za a hadu a magance matsalolin tsaron kasar da suka hana wasu yankunan Nijar zaman lafiya.