1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan adawa sun gudanar da zanga-zanga a Ghana

September 17, 2024

'Yan adawa a Ghana sun gudanar da zanga-zanga domin kalubalantar abinda suka kira yunkurin jam'iyya mai mulki na kitsa magudi a zaben kasar da ke tafe.

https://p.dw.com/p/4kjYg
Ghana Wahlen I John Dramani Mahama  und Mahamudu Bawumia
Hoto: Nipah Dennis/AFP/Getty Images, Olympia de Maismont/AFP

Dubban magoya bayan jam'iyyar adawa a Ghana sun gudanar da zanga-zanga a ranar Talata suna masu bukatar hukumar zaben kasar ta fitar da jerin sunayen 'yan takarar da ta tantance kafin zaben shugaban kasa na watan Disamba mai zuwa saboda abinda suka kira yunkirin jam'iyya mai mulki na tafka magudi. 

Karin bayani: Ghana: Zaben fidda gwani na Jam'iyyar NPP

Masu aiko da rahotanni sun ce masu zanga-zangar da suka fito a daukacin sassan fadin kasar sun yi ta daga kwalaye masu dauke da rubutun cewa 'hukumar zabe ta dakatar da yunkurin magudi' sannan kuma suna furta kalmomin cewa 'muddin ba a yi ba adalci a zabe to ba bu zaman lafiya'.

Jam'iyyar adawa ta NDC wace ta kira zanga-zangar ta dau alwashin ci gaba da gudanar da jerin gwano har sai bukatarta ta biya domin kore shakku kafin zaben da 'yan Ghana suka dade suna jira.

Karin bayani: Rikici ya kunno kai bayan bacewar kaya a hukumar zaben Ghana

Sai dai a nata bangare hukumar zaben Ghana da musanta wannan zargi inda ta bukaci 'yan adawar da su bi hanyoyin tattaunawa don samin masalaha a maimakon fantsama kan tituna.