1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ce ce ku ce kan zaben kasar Masar

June 23, 2012

Hukumar zaben kasar Masar ta ce za ta bayyana sakamakon shugaban kasar a ranar Lahadi

https://p.dw.com/p/15KQ0
Supporters of Muslim Brotherhood's presidential candidate Mohamed Morsy hold up a poster of Morsy during a demonstration against the delay of the Egyptian presidential results and against the Supreme Council for the Armed Forces (SCAF) at Tahrir square in Cairo June 22, 2012. Egypt's military rulers dismissed complaints from protesters on Friday that it was entrenching its rule and blamed Morsy for stirring up emotions that drew thousands onto Cairo's Tahrir Square. Morsy shot back that the generals were defying the democratic will of the people and said protests would go on. But he stopped short of repeating a claim to have won last weekend's election, urging simply a rapid announcement of the result, and praised the army as "patriotic". REUTERS/Asmaa Waguih (EGYPT - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Hoto: Reuters

Shugaban hukumar zaben Masar Farouk Sultan ya karyata rahotannin cewa hukumarsa za ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da ake takaddama a kai idan an jima.Shugaban hukuman ya fada wa gidan talabijin na kasa cewa har yanzu hukumar tana kokarin gudanar da bincike kan kurakuran da abokan hammayar biyu suka yi zargin an tafka.Haka nan kuma hukumar ta ce za'a bayyana wannan sakamakon ranar Lahadi amma kuma za'a ci gaba da wannan bincike har sai an tantance duk wasu bayanai an kuma yanke hukunci.

Daga farko dai hukumar ta yi niyyar bayyana wannan sakamako tun ranar Alhamis da ta gabata, amma ta jinkirta yin hakan bayan da dan takarar jamiyyar 'yan uwa Musulmi Mohammed Mursy da tsohon Frime Minista Ahmed Shafiq, suka gabatar da korafe-korafe akalla 400 a wuraren jefa kuri'u 100 a duk fadin kasar.Wannan jinkiri ne kuma kawo yanzu, ya yi sanadiyyar komawar masu zanga-zanga dandalin Tahrir inda suke bukatar ganin an yi adalci wajen ba da wannan sanarwa a maimakon makarkashiyar ci gaba da rike mulkin da suke zargin majalisar sojin kasar da kullawa.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Halima Balaraba Abbas