1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Canza rigar dakin Ka'aba a Makka

June 10, 2013

A ko wace shekara hukumomin Saudi Arabiya na canza rigar dakin Ka'aba dake birnin Makka, shin ina ake saka wannan riga kuma me ake da tsohuwar rigar da aka fitar?

https://p.dw.com/p/18nGD
epa02992433 Muslim pilgrims perform Friday prayer around the holy Kaaba in the center of the Haram Sharif Great Mosque, on the first day of the Muslim's Haj 2011 pilgrimage, in Mecca, Saudi Arabia, 04 November 2011. According to the Muslims holly book the Quran, the Kaaba was built by Abraham and his son Ismael, after Ismael had settled in Arabia. Millions of Muslims arrived in Saudi Arabia to perform their Hajj. The Hajj 2011 is due to take place from 04 to 09 November. EPA/AMEL PAIN
Hoto: picture-alliance/dpa

Rigar Dakin Ka'aba ko kuma Kiswa ko wace shekara ake canza ta. Ana canza ta duk ranar Tara ga watan Zul-Hijja.

Baki daya nauyinta ya kai kilo 820 daga cikin wannan kilogram 670 nauyin yadin ne tsantsa, sai kuma zinariya na da nauyin kilo 120 azurfa na da nauyin kilo 30.Kyallaye har 14 ne ake harhadawa domin dinka rigar Kiswa ko wane kyalle na da tsawan mita 14, da kuma fadin sentimeta 95 wato kusan mita daya.

A jimilce, kan kudin sayen kyallayen 14, da kudin dinki, da na zinariya da azurfa dake ciki ana kashe tsabar kudi Riyal fiye da miliyan 17, wato fiye Euro miliyan ukku wajen canza sabuwar rigar dakin Ka'aba.

Har zuwa shekara 1927 wato shekaru 86 kenan baya, a kasar Masar ake saka rigar Kiswa. Daga shekara 1926 ne Sarki Abdel-Aziz Al-Saoud, ya ba da izinin kafa masana'antar da za ta dinga dinka rigar Ka'aba, to amma bayan shekaru 10 aka rife wannan masaka.

Sai kuma shekara 1962 Sarki Faysal bin Abdelaziz Al Saoud ya sa aka sake kafa wata masaka a garin Umm-al-Joud, domin a dinga saka Rigar Dakin Kaaba a ciki. Wannan masaka ta fara aiki a shekara 1976

Source News Feed: EMEA Picture Service ,Germany Picture Service Muslim pilgrims circle the Kaaba and pray at the Grand mosque during the annual haj pilgrimage in the holy city of Mecca October 23, 2012, ahead of Eid al-Adha which marks the end of haj. On October 25, the day of Arafat, millions of Muslim pilgrims will stand in prayer on Mount Arafat near Mecca at the peak of the annual pilgrimage. REUTERS/Amr Abdallah Dalsh (SAUDI ARABIA - Tags: RELIGION)
Hoto: Reuters

A ko wace shekara, masakar na saka riguna biyu. Mutane 200 ke aiki a Masakar dake saka rigar Kiswa, su dukansu kwararru ne ta fannin saka, kuma hukumomin Saudi Arabiya ne suke nada su, sannan dukansu 'yan kasar Saudi Arabiya ne.

Akwai hukuma ta mussamman wadda ke kula da tsafin rigunan Kaaba.Ana yanyanka wannan riguna ne kyalle-kyalle,ana bada su kyauta ga manya-manyan baki ko kuma da wasu kungiyoyin addinin Islama.

Bugu da kari ana amfani da wasu kyallayen da aka yanka domin kayatar da wasu ofisoshin gwamnati, kokuma ofisoshin jikadancin Saudi Arabiya da ke kasashen duniya.

A shekara 1982 Saudi Arabiya ta bada kyautar wani kyalle na tsohuwar rigar Ka'aba ga Majalisar Dinkin Duniya da sunan duk al'umar musulmi na duniya.An shirya gagaramin biki wajen karbar wannan kyauta, kuma a yanzu haka Majalisar Dinkin Duniya ta lika wannan kyalle a babban dakin karbar baki na ofishin wakilan kasashe dake Majlisar.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal