Canjin sheƙa na 'yan siyasa a Najeriya
January 30, 2014Talla
Shakka babu jama'ar ƙasar na lura sau da kafa halin da lamarin siyasar na Najeriya yake cike, wanda bayan canji sheƙa na Shekarau ɗin, wasu 'yan majalisun dattawa guda 11 tare dawasu gwamnonin jihohi uku suma suka canza sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai adawa daga jam'iyyar PDP mai mulki.
Sabbabin masu sauyin sheƙar dai sun haɗa da tsoffafin gwamnonin jam'iyyar PDP uku, Sanata Bukola Saraki, da Sanata Danjuma Goje da kuma Sanata Abdullahi Adamu.
Sauran sun haɗa da sanata Ali Ndume daga Borno, da Sanata A'isha Jumai Alhassan daga Taraba da dai sauransu.