1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cafke Asari Dokubo domin amsa tambayoyi

February 6, 2014

Hukumar tsaro ta SSS a Najeriya na binciken madugun mayakan Niger Delta Mujaheed Asari Dokubo.

https://p.dw.com/p/1B3pF
Dokubo Asari Nigeria MEND Politik
Hoto: DW/Ubale Musa

Rundunar tsaron cikin gida ta SSS a Najeriya, ta kame madugun kungiyar tsagerun Niger Delta Mujaheed Asari Dokubo.

Dokubo dai na zaman kan gaba ga batun kokarin kare muradin shugaban kasar a zaben shekara ta 2015, mutumin kuma da aka ruwaito yana fadin sama da kasa za su hadu in har aka nemi hana shugaban tsayawa takara a zabukan kasar na badi.

Ana dai kallon kamen nasa da har ya zuwa yanzu hukumar ta SSS ba ta baiyana hujjar ta ba, na da nasaba da kokarin rage zaman dar-dar da tashe tashen hankulan da ke neman mamaye fagen siyasar kasar a yanzu haka.

A cikin makon jiya ne dai hukumar ta kame tsohon ministan babban birnin tarayya na Abuja da yace hanyar kwace mulki a kasar a badi dai na zaman ta tashin hankali.

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Saleh Umar Saleh