1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buƙatar yin kwaskwarima ga hukumar EFCC

October 27, 2011

Majalisar wakilan Najeriya ta bayyana buƙatar gwamnati ta gudanar da kwaskwarima ga hukumar yaƙi da ta´annaci da dukiyar ƙasa ta hanyar naɗa tsofan alƙali a matsayin shugaban EFCC

https://p.dw.com/p/130N7
Hoto: DW

Yayin da Majalisar wakilan tarayyar Najeriya ke neman a sauya shugabancin hukumar yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa da aka fi sani da EFCC don naɗa alƙalin kotun ƙoli a matsayin shugaba ƙungiyoyin fararen hula da masu yaƙi da cin hanci sun bayyana ra'ayoyinsu.

Dokar da ta kafa hukumar yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annuti a tarayyar Najeriya da aka fi sani da EFCC ta tanadi cewa ma'aikacin hukumar tsaro da ya yi ritaya ko ya ke kan aiki shine zai shugabanci hukuma,r wanda yanzu tayi ƙaurin suna tsakanin ‘yan siyasar ƙasar.

Da dama daga ‘yan siyasar da talakawan ƙasar dai na kallon wannan hukuma a matsayin Karen farautar da gwamnati mai ci ke amfani da ita wajen cimma burin danƙwafar da masu adawa ko waɗanda suka zama ƙadangaren bakin tulu ga masu mulkin ƙasar.

Wannan kuma na daga cikin dalilin da ya sa wasu ‘yan majalisar walikan gabatar da ƙudiri na neman canza dokar da ta tanadi wanda za'a naɗa ya jagoranci tun da suna zargin shugabancin yanzu da bada kai bori ya hau wajen cin zarafi ko muzgunawa waɗanda ba su miƙa wuya ga gwamnati mai ci ba.

Wannan yasa ƙungiyoyin fararen hula da na yaƙi da cin hanci tofa albarkacin bakinsu dangane wannan aniya ta ‘yan majilisar wakilai.

Yayin da wasu ke ganin wannan matakin ba zai haifar da wani cenji ba, a yaƙin da ake yi da cin hanci a ƙasar wasu kuma na ganin naɗa alƙalin kotun ƙoli zai taimaka wajen samun nasarar yaƙin.

Malam Magaji Halilu na ƙungiyar Corruption Free Society na ganin naɗa alƙalin kotun ƙoli a matsayin shugaban hukumar zai taimakawa gaggauta yin shari'a da yanke hukunci ga waɗanda ake tuhuma da cin hanci.

Sai dai wasu kamar Barrister Muhammad Mailumo wani ma gwagwarmayar kare haƙƙin bani Adama na ganin ba'a nan take ba wai an danne bodari kai, a ganin sa samun mai tsoron Allah shine kawai mafita ba naɗa tsohon alƙalin kotun ƙoli ba.

Ya ƙara da cewa yawancin tsofin alƙalan da ake son naɗawa shekarunsu sun ja da wuya su iya irin wannan aiki dake bukatar faɗi ta shi a irin shekarun su.

Masu fashin baƙi kan harkokin yau da kullum kamar Ibrahim Baffa wanda aka fi sani da Middle Bujua na ganin matuƙar gwamnati ba ta cire hannunta aka bar hukumar ta yi aikin ta ba tare da sanya siyasa ko wata manufa ba to duk wani canji da aka yi a na shugabanci ba zai haifar da alheri ko nasarar da ake son cimma ba.

Wasu masharhanta kuma na ganin a baya an kamanta nada tsofin alƙalan a hukumar yaƙi da cin hanci ta ICPC amma har ya zuwa yanzu hukumar bata kamanta kama masu mulki da suka haɗa da ministoci ko tsofi gwamoni kamar yadda EFCC take yi ba saboda haka suke ganin babu buƙatar sake wannan tsari.

Za ku iya sauraran rahoton da Al-Amin Suleiman Mohammed ya rubuta game da wannan batu

Mawallafi: Yahouza Sadisou Madobi

Edita: Zainab Mohamed Abubakar