1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burundi ta aike da taimakon soji izuwa Darfur

December 26, 2005
https://p.dw.com/p/BvEw

A karon farko mahukuntan kasar Burundi sun aike da wasu sojin kasar 10, izuwa yankin Darfur na kasar Sudan don taimakawa wajen wanzuwar zaman lafiya a yankin.

A cewar kakakin rundunar sojin kasar, wato Adolphe Manirakiza, jamian sojin zasu gudanar da aikin ne a matsayin masu sa ido a karkashin laimar kungiyyar Au .

Wadannan jamian soji a cewar kakakin rundunar sojin na Burundi an zabo sune daga cikin tsoffin hannu da sabbbin jini a cikin sojojin kasar, wanda hakan ke a matsayin wani mataki na taka rawa a siyasar kasa da kasa, bayan kaw9o karshen yakin basasar kasar na tsawon shekaru 12.

Ya zuwa yanzu dai kungiyyar hadin kann kasashen na Afrika nada jami´ai da yawan su ya tasamma dubu 7 da dari 800 dake gudanar da

aiyuka iri daban daban na yankin na Darfur don ganin cewa an samu kwanciyar hankali da lumana