1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burundi: Soja sun sanar da yin juyin mulki

Mouhamadou Awal BalarabeMay 13, 2015

Wani hafsan sojan kasar Burundi ya bayyana cewa sun hambarar da shugaba Pierre Nkurunziza daga karagar mulki sakamakon yunkurinsa na yin tazarce.

https://p.dw.com/p/1FPDK
Pierre Nkurunziza
Hoto: I.Sanogo/AFP/GettyImages

Cikin wata sanarwa da ya karanta a daya daga cikin barikokin soje na birnin Bujumbura, Janar Godefroid Niyombare ya ce sun rusa gwamnatin Burundi da ke ci yanzu, saboda sun kosa da izgilin shugaba Nkurunziza na kin mutunta yarjejeniyar zaman lafiya ta Arusha.

Kanfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewa tuni sojoji suka yi ma gidan rediyo da talabijin mallakar gwamnatin Burundi kawanya tare da haramta shiga da fita. Sai dai kuma wani mai bawa shugaba Nkurunziza shawara ya danganta sanarwar juyin mulkin da wasan kwaikwayo.

Shi dai shugaba Pierre Nkurunziza ya na kasar Tanzaniya yanzu haka don halartar taron koli da shugabannin kasashen yankin gabashin Afirka ke gudanarwa, da nufin warware rikicin da kasarsa ke fama da shi. 'Yan adawan Burundi sun zargin Nkurunziza da take yarjejeniyar da ta bayar da damar kawo karshen yakin basasan da kasar ta yi fama da shi, wanda ya tanadi wa'adin mulkin biyu kacal.