Burtaniya ta kara sanya wa Rasha takunkumi saboda Ukraine
February 23, 2025Burtaniya ta sanar da wani sabon takunkumi ga Rasha a daidai lokacin da aka cika shekaru 3 cif da mamayar da ta fara yi wa Ukraine, a wani mataki na kara dakile mata hanyoyin samun kudaden shiga.
Sakataren harkokin wajen Burtaniya David Lammy ya ce zai sanar da sabon takunkumin a nan gaba, kuma za su ci gaba da aikin hadin gwiwa da Amurka da kuma sauran kawayensu na Turai don cimma masalahar dakatar da yakin, amma fa tilas ne a sanya Ukraine cikin tattaunawar.
Karin bayani:Rasha ta tafka asarar dubban sojoji a Ukraine - Burtaniya
Ya kara da cewa Burtaniya za ta ci gaba bai wa Ukraine agajin Fam biliyan 3 a shekara domin kare kanta daga Rasha a fagen yaki, kuma a shirye kasarsa take ta aike sojojinta domin aikin wanzar da zaman lafiya a kasar idan har akwai bukatar hakan.
Karin bayani:Rasha ta yi wa Burtaniya barazana kan Ukraine
A gefe guda kuma Rasha ta sanar da kakkabo jirage marasa matuka guda 20 da Ukraine ta kai mata hari da su a yankunanta guda 6 a Lahadin nan.