1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso ta kore batun dauko sojoji daga Rasha

October 27, 2022

Kafin yanzun dai akwai wadanda ke nuna damuwa ne game da take-taken hukumomin Burkina Faso na dauko sojojin hayar Wagner na Rasha, kamar yadda makwabciyarta wato Mali ta yi.

https://p.dw.com/p/4IjYs
Burkina Faso | PK Ibrahim Traore
Hoto: AA/picture alliance

Shugaban gwamnatin rikon kwarya a Burkina Faso, Keftin Ibrahim Traore, ya ce kasarsa ba ta da aniyar gayyato sojojin haya musamman daga Rasha a yaki da kasar za ta karfafa da mayakan tarzoma.

Keftin Traore ya shaida wa wata tawagar manyan jami'an diflomasiyyar Amirka ne da suka ziyarci Ouagadougou babban birnin kasar.

Kafin yanzun dai akwai wadanda ke nuna damuwa ne game da take-taken hukumomin Burkina Fason na dauko sojojin hayar Wagner na Rasha, kamar yadda makwabciyarta wato Mali ta yi.

Wata jami'ar da ke aiki karkashin sakataren kula da al'amuran siyasar duniya a Amirka, Victoria Nuland, ta fada a jiya Laraba cewa lamuran tsaro sun kara sukurkucewa a Mali bayan shigar sojojin hayar Rashan, tana mai zargin karuwar take hakkin bil adama.

Ita ma dai Majalisar Dinkin Duniya ta nunar da karuwar matsalar ta take hakkin bani Adaman a Mali a baya-bayan nan.