1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso: Dakatar da RFI a kasar

December 3, 2022

Majalisar mulkin Soji a Burkina Faso ta dakatar da shirye-shiryen kafar yada labarai mallakin Faransa ta RFI a kasar.

https://p.dw.com/p/4KRRV
Kafar yada labarai ta RFI
Hoto: Yoan Valat/epa/dpa/picture alliance

Dakatar da kafar RFI a Burkina Faso na zuwa ne sakamakon tuhumar da ta yi wa kafar na yada labaran bogi da kuma ba 'yan ta'adda damar fadin albarkacin bakinsu.

A cikin sanarwar da gwamnatin sojin kasar ta fitar, ta ce ta dauki matakin ne na dakatar da kafar daga yada shirye-shirye a kasar sakamakon jawabin barazana ga al'umma na shugaban wata kungiyar 'yan ta'adda da kafar ta yada a wannan Asabar din.

Sanarwar ta kuma karyata rahoton kafar RFI wanda ya nuna cewa shugaban mulkin sojin kasar Kaptin Ibrahim Traore, wanda ya kwace ikon kasar a watan Satumbar da ya gabata ya yi ikirarin cewa wasu sun yi yunkurin yi masa juyin mulki. Har kawo yanzu, kafar yada labaran bata ce komai dangane da dakatarwar ba.