1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari ya halaka sojojin Burkina Faso

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 28, 2022

Wani harin ta'addanci da masu da'awar jihadi suka kai a Burkina Faso, ya halaka sojoji sama da 10 tare da jikkata mutane kusan 30. Hukumomi sun nunar da cewa, 20 daga cikin wadanda suka jikkatan sojoji ne.

https://p.dw.com/p/4HThD
Benin | Ta'addanci | Hare-Hare
Burkina Faso na fama da hare-haren ta'addanciHoto: Marco Simoncelli/DW

Rahotanni daga mahukuntan kasar na nunar da cewa, kawo yanzu fararen hula 50 ne suka yi batan dabo. 'Yan ta'addan, sun kuma yi yunkurin kai hari kan wani ayarin motoci da ke kan hanyarsu ta kai kayan masarufi birnin Djibo. Ana dai fargabar adadin wadanda suka halaka ka iya karuwa zuwa mutane 60, a kasar da ta kwashe sama da shekara guda tana fuskantar hare-haren ta'addanci daga masu dauke da makamai da ke da alaka da kungiyar 'yan ta'addan IS da al-Qa'ida.