1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso: An hana yawon dare da babura

Gazali Abdou Tasawa
September 20, 2018

Gwamnatin Burkina Faso ta kaddamar da dokar haramta yawon dare ga wasu ababan hawa masu kafa biyu ko ukku a yankin gabashin kasar inda kungiyoyin masu da'awar jihadi suka yawaita kai hare-hare

https://p.dw.com/p/35DAO
Burkina Faso, Ouagadougou, Motorräder
Hoto: DW/Christine Harjes

Gwamnan yankin Gabashin kasar Kanal Ousmane Traore ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. 

Dokar za ta yi aiki daga karfe bakwai na yamma zuwa karfe biyar na safe. Sai dai kuma gwamnan ya ce matakin ya tanadi tsaurara bincike kan sauran motocin fasinja da na daukar kaya wadanda dokar ba ta haramta masu ci gaba da zirga-zirgar ba. 

Kazalika matakin ya tanadi ci gaba da rufe wuraren hako ma'adanai a gargajiyance wadanda ke aiki da ababe masu fashewa kirar gargajiya wadanda sau tari aka yi amfani da su wajen kai hari kan jami'an tsaro a watanni baya bayan nan a kasar.