Bunƙasa dangantaka tsakanin Jamus da Masar
April 19, 2011Ministan kula da harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya isa birnin al-Qahira na Masar domin tattauna batutuwan da suka shafi siyasa tare da jami'an ƙasar, watanni tara kenan bayan masu rajin tabbatar da dimokraɗiyya a ƙasar suka tilastawa shugaba Hosni Mubarak yin murabus. Gwamnatin Jamus dai tana bayar da tallafin kuɗin daya kai Euro miliyan 50 a duk shekara ga ƙasashe irin su Masar da Tunisia domin taimaka musu bunƙasa sha'anin dimoƙraɗiyya ta hanyar gurabun ƙara ilimi da kuma shirye-shiryen baiwa 'yan ƙasar horo a fannonin ayyukan su.
A lokacin ziyarar dai, Guido Westerwelle zai gana tare da wakilan majalisar wucin gadin da ke gudanar da harkokin mulki a ƙasar ta Masar da kuma majalisar kula da haƙƙin bil'adama a ƙasar. Tunda farko ministan harkokin wajen na Jamus Guido Westerwelle ya bayyana cewar Masar za ta taka muhimmiyar rawa akan batun ko zanga-zangar neman sauye-sauyen dake gudana a ƙasashen larabawa daban daban za su kasance tubalin girka tsarin dimoƙraɗiyya mai ɗorewa a yankin.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman