1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukin juyayin hare-haren Hiroshima a Japan

August 6, 2010

Amurka, Britataniya da Faransa sun aike da Jakadunsu zuwa Hiroshima

https://p.dw.com/p/OdOx
Hoto: AP

A birnin Hiroshima na ƙasar Japan, ana bukin cika shekaru 65, da harin Nukiliya na farko a Duniya, inda Amurka a karon farko ta aike da wakilinta.  Japan data kasance ƙasa ɗaya tilo da aka taɓa kaiwa irin wannan harin dai, tasha kira da a haramta makaman Atom a Duniya. An kiyasta cewar, mutane dubu 140 ne suka rasu nan take ko kuma suka nakasa daga matsananciyar ƙuna nan take a sakamakon  harin bomb din na Hiroshima, ayayinda wasu dubu 70 suka mutu daga harin makamin Nagasaki, kwanaki uku bayan nan. Amurkan dai bata taɓa nadamar waɗannan tagwayen hare-hare ba. Ayayinda wasu Amurkawa ke ganin cewar, hare-haren sun zame wajibi a wancan lokacin ne, domin gaggauta kawo karshen yaƙin Duniya na biyu, wasu kuwa sunce harin bashi da dalili in bada wata kila gwajin makamai.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Edita: Umaru Aliyu