1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar Turkiya

March 16, 2012

Turkiya ta bukaci ba da karin kariya ga yan gudun hijirar Siriya

https://p.dw.com/p/14LlS
Turkey's Prime Minister Recep Tayyip Erdogan addresses the lawmakers of his Islamic-rooted party at the parliament in Ankara, Turkey, Tuesday, Feb. 7, 2012. Erdogan, calling the veto at the UN Security Council a "fiasco" said his country can't remain silent to the massacre of Syrian people and will continue to support the Arab League efforts. "We will launch a new initiative with countries that standby the Syrian people instead of the regime," Erdogan said without elaborating. (Foto:AP/dapd)
Shugaba Reccep Tayyip ErdoganHoto: AP

A sakamakon karuwar yawan 'yan gudun hijrar Siriya da ke kwarara zuwa Turkiya, fraiministan kasar, Reccep Tayyip Erdogan ya bayyanar da bukatar kebe wani yanki kusa da iyakar kasashen biyu domin kare 'yan gudun hijrar. Erdogan ya kara cewa zai janye jakadansa daga Siriya da zaran mutanen kasarsa sun bar kasar. Ma'aikatar harkokin wajen Turkiya ta yi kira ga dukan 'ya'yanta da ke Siriya da su fice daga wannan kasa. A dai halin yanzu kasashe mambobin kungiyar hadin-gwiwar yankin Gulf sun rufe ma'aikatun jadancinsu da ke birnin Damaskus. A cikin wata sanarawar hadin-gwiwa da suka bayar sarakunan kasashen yankin Gulf guda shida sun soki Shugaba Bashar al Assad da kashe al'umar kasarsa da kuma yin fatali da duk wani shiri na samun mafita daga rikicin siyasar kasar. Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutane dubu 8 suka rasa rayukansu a kasar ta Siriya tun bayan ta boren nuna adawa da gwamnati shekara guda da ta gabata.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi