1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron zaman lafiya na sarakunan gargajiya a Lagos

November 21, 2022

Sarakunan arewacin Najeriya sun je Lagos, inda suka gudanar da wani taron fadakarwa ga al'umma a kan samar da zaman lafiya gabanin babban zaben kasar da ke tafe.

https://p.dw.com/p/4JqBy
Nigeria Ramadan
Hoto: picture-alliance/AP Photo/G. Osodi

Babban burin sarakunan da suka halarci taron shi ne fadakar da jama'a kan bukatar guje wa amfani da kalamai da ka iya haifar da tashin hankali a yayin yakin neman zabe da kuma lokacin zabukan da za a yi a watan Fabrairun 2023.

Sarkin Hausawa na Lagos Alhaji Aminu Dogaro ya ce siyasa ba da gaba ba indai ana bukatar zaman lafiya ita ce mafita.

Alhaji Muhammad Banbado, Sarkin fulanin kudu maso yammacin Najeirya, ya ce siyasar addini ko kabilanci ba ta dace ba a kasa kamar Najeriya.