1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Mika mulki ga gwamnatin riko

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 4, 2021

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci Janaral Abdel Fattah al-Burhan jagoran juyin mulkin da aka yi a Sudan, ya koma kan tsarin mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/42bUB
Putsch im Sudan | General Abdel Fattah al-Burhan
Jagoran juyin mulkin Sudan, Abdel Fattah al-BurhanHoto: /AP/dpa/picture alliance

Sakatare janar na Majalisar ta Dinkin Duniya Antonio Guterres ya kuma bukaci jagororin juyin mulkin na Sudan, su tsara hanyoyin kafa gwamnatin rikon kwarya. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin sakataren na Majaliasar Dinkin Duniya ya fitar, inda ya ce Guterres din ya kuma yi kira ga sojojin su sako Firaminista Abdalla Hamdok da sauran fararen hular da  jagororin juyin mulkin ke tsare da su.