1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

190811 Syrien USA EU

August 19, 2011

A ci-gaba da matsin lambar da Siriya ke fuskanta bisa ɗaukar matakan soji akan 'yan zanga-zanga, ƙasashen yamma sun yi kira ga Shugaba Assad da ya yi murabus

https://p.dw.com/p/12KOy
Wani ɓangare na masu boren nuna adawa da AssadHoto: dapd

A cikin wata shelar bai ɗaya da suka yi ƙasashen yamma da suka haɗa da Jamus da Faransa da Brtaniya sun bi sahun Amirka da Ƙungiyar Tarayyar Turai wajen haramta shugabancin da Bashar al-Assad ke wa ƙasar Yaman tare da yin kira gareshi da yayi murabus.

Da kakkausan harshe ne dai Amirkan da Ƙungiyar Tarayyar Turai(EU) suka yi kira ga Shugaba Bashar Al-Assad na Siriya da ya yi murabus abin da da yawa daga cikin masu sa ido akan yadda al'amura ke wakana a ƙasar ta Siriya suka ce wani sabon mataki ne. A ma makon da ya gabata sai da ƙasashen irinsu Saudiya da Masar suka yi suka ga gwamnatin Shugaba Assad.

Ra'ayin ƙwararre kan matakin Amirka da EU

A cikin hirar da Aljazeera ta yi da shi, Fawaz Gerges ƙwararren masani akan al'amuran yankin Gabas ta Tsakiya da ke zaune a birnin London ya nuna irin tasirin da wannan mataki ka iya yin akan gwamnatin Siriya a cikin gaggawa.

" Manufar wannan matsayi da Amirka da Ƙungiyar Tarayyar Turai suka ɗauka ita ce yin haɗin -gwiwa tsakanin gaggan ƙasashen yamma da na yankin Gabas ta Tsakiya wajen mayar da gwamnatin Assad saniyar ware. A haƙiƙa yanzu an ƙaddamar da yaƙi kan gwamnatin Siriya. Kuma babu shakka wannan haɗin kai tsakanin zai yi tasiri akan Siriya nan ba da daɗewa ba. "

Akan haka ne ma Shugaba Barack Obama ya ba da umrnin haramta sayen man fetur daga ƙasar ta Siriya tare da kuma hana Siriyar taɓa kadarorinta da ke Amirka da kuma haramcin yin cinikayya ko kuma zuba jari tsakanin Amirkawa da gwamati ko kuma ƙasar ta Siriya.

Matsayin 'yan Siriya da ke waje

Jordanien Syrien Demonstration in Amman gegen Präsident Bashar Assad
Matan Siriya da ke a Jordan riƙe da tutar 'yanciHoto: dapd

Su kuma dai 'yan ƙasar ta Siriya da ke samun mafaka a waje suna ci gaban da bin kadin abin da ke wakana a ƙasar. Lubna Mounir 'yar ƙasar Siriya ce da ta nemi mafaka a Jordan.Ta ce:

" Tun watanni biyar da suka gabata ne ake zud da jinin al'umar Siriya. To amma yanzu gamayyar ƙasa da ƙasa ta sa baki . Ko da yake makkoni biyu kacal bayan ta da bore a Masar ne ƙasashen duniya suka tsoma baki a kasar, to amma duk da haka mun gamsu da matakan da ake ɗauka muna kuma sa ran ganin a ci gaba da hakan.

Komitin kare hakkin bil Adama na Majalisar Ɗinkin Duniya shi kuma ya ce zai bincike cin zarafin da aka yi wa farar hula a ƙasar ta Siriya tare da shigar da ƙara a kotun hukunta miyagun laifuka ta ƙasa da ƙasa. Akalla mutane dubu biyu suka rasa rayukansu bayan ƙaddamar da bore a ƙasar ta Siriya, waɗanda akasarinsu suka gamu da ajalinsu a cikin hare-haren da sojoji suka rinka kaiwa ta sama da ƙasa da kuma harbe da harbe.

Martanin gwamnatin Siriya kan matakin Amirka da EU

Gwammatin Siriya ta mai da martani game da matakin da Amirka da Ƙungiyar Tarayyar Turai suka ɗauka ta bakin ministan watsa labaranta, Reem Haddad wanda ya ce shugaba Obama da sauran ƙasashen yamma za su kara rura wutar wannan rikici a maimaikon ba da taimako wajen yin gyare-gyaren da shugaba assad ya ba da sanarwar aiwatar da su a baya-bayan nan - abin da 'yan adawa suka ce yaudara ce kawai.

Syrien Militär
Sojoji masu murƙushe boren adawa da gwamnatiHoto: AP

Fawaz Gerges, na makarantar kimiyar tattalin arziƙi da siyasa da ke birnin London ya bayyana shakku game da samun nasarar matsin lambar da gamayyar ƙasa da ƙasa ke wa gwamnatin shugaba Assad.

"Shugaba Assad yana yaƙi ne domin ganin ya ci gaba da jan ragamar mulki. Abin takaici shi ne babu abin da zamu shedar in banda ci gaban taazzarar wannan rikici ta fannin siyasa da tattalin arziƙi da kuma aikin soji nan da 'yan kwanaki. Gwamnatin Siriya za ta ci gaba da yaƙi har sai ta ga abin da ya ture wa buzu naɗi. Wannan gwamnati, gwamnati ce ƙarfaffa da ke samun ɗaurin gindi a cikin gidan Siriya, take kuma mallakar makamai masu illa da za ta iya yin amfani da su."

Ko a ranar 19.08.2011 sai da dakarun ƙasar ta Siriya suka halaka mutane 19 yayin zanga-zangar da aka gudanar bayan sallar juma'a- abin da ke nuna ga saɓa alƙawarin da Assad ya ɗauka a ranar 18.08.2011 cewa z a a daina ɗaukar matakan soji akan farar hula. A wani ci gaban kuma ƙasashen Rasha da Turkiyya sun yi fatali da kiran da ƙasahen yamma ke wa shugaban na Siriya da ya sauka daga karagar mulki.

A kasa za ku iya sauraron wannan rahoto da rahoton da Wakilinmu Mahmud Yahaya Azare ya aiko mana akan tsamin dangantakar Masar da Israila.

Mawallafi: Juergen Stryjak/Halima Balaraba Abbas
Edita: Zainab Mohammed Abubakar