Brexit: EU ta ce bakin alkalami ya bushe
February 4, 2019Talla
Tarayyar Turai ta ce ba za ta sake waiwayen yarjejeniyar ficewar Birtaniya daga gamayyar kasashen kungiyar ba, ciki har da matsayin yankin nan na Ireland mai sarkakiya.
Sai dai babban mai shiga tsakani kan batun ficewar Birtaniyar daga kungiyar Michel Barnier wanda ya sanar da a wannan Litinin, ya ce akwai yiwuwar samun mafita kan batun ficewar kasar.
A ranar 29 ga watan gobe ne dai Birtaniyar za ta fice daga kungiyar, koda yake majalisar dokokin kasar ba ta amince da batun iyakar Ireland ta Arewa da jamhuriyar Ireland ba.
Matsalar dai ita ce batun shige-da-fice a iyakar Jamhuriyar Ireland wadda za ta ci gaba da zamanta cikin kasashen Turan, yayin da Ireland ta Arewa ke cikin Birtaniya.